Ko shakka babu jiharmu na fuskantar wani bubban kalubale a wannan lokaci da muke ciki, lamarin da ke bukatar ci gaba da ayyukan zaman lafiya tare da bunkasa, wanda gwamnatin Makarfi ta iya cimmawa cikin shekaru takwas din da suka gabata.
Kawo yanzu dai mun kai ga wani matsayi ga kudurin da muka sanya a gabanmu, inda zamu sanar da ku, ko mu su wanene, da kuma inda muka fito, da inda muke, yanzu da inda muka dosa daga nan, da kuma irin burin da muke da shi, a rayuwarmu.
A halin yanzu dai mun bar yanayi na ‘yan kururuwar shaida da masu sarka banbanci irin na addini, da bautarwa, da yayata kalaman rudu, fuskar zamantakewar al'ada, da nakasa imani, da yamutsa tsarin tattalin arzaki, da siyasar koma-baya, dajuya tunani, da haifar da rudanin hankali, da talauci, wanda kan tada hankali, da yamutsa shaanin karatu, da bata basira, da ci gaba da aikata rasha wa, gami da rashin tsaro.
A nan, muna da bukatar jagora wanda keda kaifin basirar ci gaba da kyautata rayuwarmu wanda kuma zai iya jagorantarmu a wannan ka sa tamu.
A nan mun yi imani a kan cewa Arc. Namadi Sambo, nada wada nnan kyawawan halaye, da suka cancanci ya zama mana gwamna a ranar 29 ga watan mayun shekarar 2007.
A. KARBUWA
Ya zama wajibi gwamnanmu ya zama mutun karbabbe ga al'umman mari rinjaye. Hakan kuwa ya taso ne sabili da irin banbanci da yanayin mu, haka kuma ya zama wajibi ya zame karbabbe ga sauran al'ummu, wadanda ba a cikin jiharmu suke ba, ciki kuwa har dana kasashen waje.
Irin wannan mutum ya kamata ya kasance na kowa, wanda ka iya bugun kirji yayi mu'amulla da rukunin mutane daban daban, ba tare da yin laakari da matsayinsu ta rayuwa ba, ko yanayi na addini, kotsarin zamantakewarsu, da kabilu, gami da kasarsu ba, WANNAN MUTUM KUWA SHI NE ARC. NAMADI SAMBO.
B. IMANI
Muna da bukatar gwamna wanda yayi Imani da Allah, Irin wannan jagora ya zama wajibi, ya kaucewa aikata hakan a baki, ko kuma na jeka-na-yi-ka-ba, wato wanda bai da cikakken tsoron Allah a zuci.
Ya wajaba gwamnanmu ya zama mai godiya ga ubangiji, tare da dukufa ga jagoranci irin na Allah, kuma irin wannan jagora ya kamata ya rika tuna ubangiji ga dukkan ayyukansa na yau da kullum, wanda ko tantama babu irin wannan mutum shine Arc. Namadi Sambo.
C. KWARIN GUIWA
Gwamnanmu, ya zama wajibi, ya zama mai kwarin guiwar jagorantarmu a kowane irin hali, kuma a kowane irin yanayi.
Baya ga tsoron uban giji irin gwamnan da muke bukata, ya za ma wajibi ya kasance mara tsoro, don ya yi mana kyakkyawan jagoranci, don amfanin jihar a kowane irin yana yi kuwa.
Irin wannan gwamna, ya kamata ya zama mai ikon fada-a-ji, tare da yin bakin kokarinsa, don amfanin jihar, batare da zama dan-amshin-shatar-wani; mutum; ko kuma wasu mutane ba, Wannan kuwa shine ARC. NAMADI SAMBO.
D. Daidaito
Munada bukatar gwamna wanda ke duban kowane dan asalin jihar, dama wanda ba dan asalin jiha ba, a matsayin dan-uwa, bisa ga yin laakari da cewa dukkanmu daga uban giji muke, kuma kasarmu ta gado guda daya ce.
Irin wannan mutum bai kamata ya zame Dan-Lelen wasu al'umma tare da tauye wasu rukunin al'ummu ba. Jagoran jiha irin tamu mai kunshe da mabanban tan a;'ummu, tilas ya zame uba, kuma uwa, ga dukkan al'umma, baki, daya, ga dukkan wani batu daya shafi jiharmu.
E. CANCANTA
Irin gwamnan da muke bukata tilas ya zame, ya cancanta, kuma baya ga batun ilimi, tilas ya zame mai kaifin basira, ta yadda zai iya zama a tsanake, ya tsara dabarun da zasu sanya, a kai ga kyakkyarwar bukata. Kuma tilas a gwada shi, da kuma samun sakamako mai kyau wato irin Arc. Namadi Sambo ke nan.
F. MAI HABA-HABA
Ya zama wajibi gwamnanmu, ya zame mai yin naam da bukatun Jamaa, domin ganin mun sami jagoran jamaa, Tilas ya zame amintacce, tare da dukufa ga ayyukan Jaamaa, Kuma tilas ya kasance mai nuna haba-haba ga kowa da, tunawa da uban giji, wanda shi ne Arc. Namadi Sambo.
G. BASIRA
Muna da bukatar mutum mai basira, wanda Allah ya bashi baiwar samun nasara, ga dukkan ayyukan daya kuduri aniyar aiwatarwa.
A matsayin mutum mai basira, tilas ya rika nunakaifin hikima ga tuntakarar dukkan batutuwan da sukataso a ofishin gwamnan jiha, irin tamu, wanda shi ne Arc. Namadi Sambo.
H. KOSHIN LAFIYA
Ya zama wajibi gwamnanmu ya zame mai koshin lafiyar jiki, data hankali, don iya jagoranta jiha irin tamu, mai kunshe da mabanbantan al'ummu daban daban.
Kuma tilas ya zame mai kaifin hankali, don iya tunkarar dukkan irin matsalolin daka iya taso masa. A don hakairin wannan jagora, ya wajaba ya kasance mai hangen nesa, ta yadda zai iya yin hulda da kowace irin al'umma, a yanayi daban daban, kuma tilas ya zame mai dauriya, da hakuri. Wato irinsu Arc. Namadi Sambo ke nan.
I. MAI SON CI GABA
Muna da bukatar jagora mai son ci gaba, wanda zai iya taimakawa ga kara gina jiharmu ta Kaduna. Jagoran da muke bukata yazama wajibi ya zama, mai aiki tukuru, da himma, kuma tilas ya zame mai kaifin hankali, tare da iya kirkirar matakan ciyar da jihar gaba, fuskar bunkasar masana'antu, da kuma hada-hadar kasuwanci. Irin Arc. Namadi Sambo.
J. GASKIYA
Ya wajaba jagoranmu, ya zame mai gaskiya ga dukkan ayyukansa, tilas kumaya zame mutum wanda zai iya tsare gaskiya, ga dukkan ayyukansa, kuma bai kamata ya zama jagora, wanda bayan ya soma aiki daga bisani ba zai iya sauke nauyin da aka dibiya masa ba.
Ya zama tilas ya zama mai fada da cikawa, tare da tsare matsayinsa, kuma tilas ya zama wanda al'umma ta dogara a kansa. Wato Arc. Namadi Sambo ke nan.
J. MASANI
Ya zama wajibi gwamnanmu ya kasance mai cikakkar masaniya, da shaidu, ga kuma gaskiya, gami da sanin kamun ludayin jagorantar jiha, mai kunshe da mabanbantan al'ummu irin tamu.
Haka kuma ya zama tilas ya kasance bashi da gefe wato ba tare da samunsa da wata inda-inda ba. Kumaya kamata ya zame masani ta yadda zai iya tantance bukatun al'umma. Irinsu Arc. Namadi Sambo ke nan.
K. MAI NUNA KAUNA
Irin jagoran da muke bukata, wajibi ya zame mai aikata alheri, da kuma rungumar Jamaa, Haka kuma tilas ya zame mai nuna tausayi ga al'umma.
Wajibi kuma, ya zame mai aikata alheri tare da rungumar kowa, gami da saurin yafewa dukkan wadanda suka saba masa, a matsayinsa na uba ga kowa. Irin ayyukansa tilas su kasance na irin mutumin dake nuna kauna, wato irin Arc. Namadi Sambo ke nan.
L. KWADAITARWA
Wajibi ne ga gwamnanmu ya zama mutum mai kwadaitarwa kan sahihi yar hanya, ta hanyar irin wannan kwadaitarwa zai iya jagorantar al'umma, kuma amatsayinsa na jagora, tilas ya sami kwarin guiwar aikata abubuwan kirki, tare da sakawa jamaa ta hanyar alheri, yadda ya kamata. Kamar dai gwarzon namu Arc. Namadi Sambo.
M. DAN KISHIN-KASA
Irin gwamnan da muke bukata, tilas ya zame mai kishin ganin kasar nan, ta ci-gaba, da zamewa dunkulalliyar kasa, kuma tilas ya zame mai kaunar kasarsa a zuci, tare da kaucewa jagoranci bisa tafarkin banbancin sashe ko kuma kabilanci.
Haka kuma wajibi ne, ya guji kare bukatun wani rukunin al'umma tare da kaucewa ko kuma yin watsi da saura, a don haka tilas ya zame cikakken dan kishin kasa a zuci, wato zancen Arc. Namadi Sambo ke nan.
N. MANUFA
Gwamnada muke bukata, tilas ya guji nuna son kai, ko zuciya, da kuma rashin manufa ga ayyukansa, a don haka gamnan damuke bukata wajibi, ya rika duban batutuwa da manufa guda, tare da fuskantar lamura bisa cancanta, ba tare da nuna wata son zuciya ba, bisa gatafarkin banbancin kabila, ko kuma addinni. Wato ha irin na Arc. Namadi Sambo ke nan.
O. KISHI
Gwamnanmu, wajibi ne, ya zame mai bada gudunmawa ga ci gaban jihar kuma wajibi ne, ya zame mai nuna kauna ga jihar, tare da kasa baki-daya, tare da zummar kula da jin dadin jama'a a zuci.
Haka kuma wajibi ya guji muzanta jiharsa, ko kuma kasarsa bisa ga kowane irin dalili.
A nan muna magana ne akan Arc. Namadi Sambo.
P. CANCANTA
Muna da bukar gwamnan da ya cancanci rike wannan mukami, kuma ya ke da dukkan abubuwan da ake bukata, na rike muhimmin ofishi irin wannan, cancantarsa a nan, ba wai muna nufin samun digirori barkatai ba, ko kuma rikon wani mukami, fiye danagwamna ba.
A nan muna nufin, cancantar zama nagartaccen-jagora, wanda ka iya sauke dukkan nauyin daya rataya a wuyansa. Haka kuma wajibi ne ya zame masani a kan zamantakewar rayuwa, tare da kwarewa da kuma basirar tantance dukkan shawarri yadda ya kamata, kafin ya yanke hukunci a kai.
Q. ZURFIN-TUNANI
Muna da bukatar jagora, mai zurfintunani, tare da yanke hukunci masu nagarta, muna da bukatar jagora dake da kaifin hankali, da kamala, tare da basirar sauraron kowane bangare, kafin daga bisani ya yanke shawarar data kamata.
Haka kuwa zai iya aukuwa ne ta hanyar samun kamulallen mutum, da zai nazarci lamura kamar yadda suke. Kuma tilas ya kasance jagoranda irin alakarsa da sauran mutane, ka iya sanyawa a san ko shi waneno, wanda kuma zai iya lalubo hanyoyin warware matsalinmu. Wato Irinsu Arc. Namadi Sambo.
R. BAWAN JAMAA
Irin gwamnan da muke bukata, wajibi ne ya kaucewa nuna giyar mulki, ga ayyukansa, a don haka muke da bukatar jagora wanda a kullum yake mika wuya ga uban giji, don yin jagoranci abin koyi. Haka kuma wajibi ne, ya zama jagora amma ba mai mulki ba, wanda ke yin aikin bautawa Jamaa, kamar yadda ya kamata.
S. AMINTACCE DA IYA TAKA TSAN TSAN
Muna da bukatar jagora wanda ayyukansa na musamman zasu hada da iya samun amintaka daga rukunin al'ummu daban daban, na wannan jiha bisa ga yanayin da zai samu karbuwa, ga kowa. Haka wajibi ne ya zame mutum amintacce, Kuma tilas ya kasance mai taka-tsan-tsan, a kan dukkan batutuwan da sukataso.
T. HADA KAI
Jiharmu, na daya daga cikin jihohin dake kunshe da dimbin mabanbantan al'umma, a Najeriya, haka kuma tana kunshe da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, dama baki, yan kasashen waje, da ba zaa iya kwatantawa da sauran jihohi ba, akasar nan,
A matsayinta na cibiyar siyasar arewacin Najeriya, kai harma da kasa baki daya, munadabukatar jagora wanda tasirinsa ya dara dogara akan kabilanci. Tauraron hadin kai, wanda dukkanmu zamu bi, don kasancewa dunkulallar al'umma a jihar, kamar yadda muke da asali daga Ubangiji.
Kuma wajibi ne ya zame mai kwarin guiwar hada-kanmu, kumashi kansa tilas ya zame jigon hadin-kai.
U. HANGEN NESA
Wajibi ne gwamnamu, ya zame mutum wanda tuni yake da masaniya a kan yadda ya kamata kasar nan ta kasance, amma ba wanda zai kwai kwayo ko kuma yin aiki akan abin da wasu suka riga suka aikata ba. Irin wannan jagora, wajibi ne ya zame mai basira tare da muradin ganin ya tafi da kowa, bisa ga irin fatar dayake da ita. Wato irinsu Arc. Namadi Sambo ke nan.
V. HIKIMA
Muna DA BUKATAR Jagora, wanda ke cike da hikima, don gan iya iya fiddamu daga irin halin da muke ciki, a dai-dai lokacin da gwarzon jagora kamar gwamna Ahmed Makarfi, ke yin ban-kwana daga mulki, muna da bukatar mutum, wanda ke da cikakkar kamala, ta yin aiki irin wanda zai biyabukatunmu.
A don haka tilas ya zame wanda ke da masani ya ko kuma sanin makamar mulki, kamar Arc. Namadi Sambo.
W. BAIWA
Munada bukatar jagora, wanda ke samun jagoranci uban giji, a kan dukkan yanayi, kuma tilas ya zame jagora, wanda ya sha gwargwamaya a bangarori daban-daban, narayuwa. Wanda har ila yau zai iya daidaituwa da kowane irin yanayi, ya-Allah na gumi, ko dari kuma wajibi ne ya kasance yana da basira ko kumahikimar rayuwa, ta masu zama a kan tsauni ko kuma a kurmi.
X. ZIMMAR TAIMOKO
Wajibi ne gwamnanmu ya kasance wanda ka iya nuna damuwa akan duk irin yanayin da muke ciki, amma ba mai nuna halin ko in kula ba.
Irin yanayin wannan da muke ciki, wajibi ne akullum ya zame ashirye gataimaka mana wanda har ila yau zamu rika zama tare dashi, a yannayi na juyayi, ko kuma farin ciki, wato mai taimako kuma amintaccen jagora. Irin Arc. Namadi Sambo.
Y. BURI / FATAH
Wajibi ne gwamnanmu ya zame mutum mai matukar nuna damuwa a game da irin matsalolin da suka shafi jihar nan, wanda kuma a ko yaushe yake kokarin kaiwa ga matakan kyautata rayuwar jama'arsa.
Irin himma da kuma burin dayake da shi, ga jihar ya kamata ta kasance to gina jihar, kamar yadda dukkanmu muke da bukata.
Wato mutum, irin Arc. Namadi Sambo.