Shi dai Arc. Mohammed Namadi Sambo, an haifeshi ne birnin zariya ranar biyu ga watan Agustan shekarar 1952, dake nan jihar Kaduna.
Ya kuma soma karatunsane a makarantar firamare ta Baptist dake Kakuri Kaduna a shekarar 1959, da kuma makarantar firemare ta kobi, dake cikin jihar Bauchi.
A tsakanin shekarar 1967 zuwa 1971, yahalarci makarantar sakandare ta zariya, wadda a yanzu ake kira kwalejin Al Huda Huda dake zariya.
A shekarar 1972 zuwa da 1973 ya halarci kwalejin share fagen shiga Jami'ah, ta Jami'ar Ahmadu Bello dake zariya.
A cikin shekarar 1973, ya samu shiga sashen zayyane zayyane na Jami'ar ta Ahmadu Bello dake zariya, inda ya kammala a shekarar 1976. Inda ya sami takardar shaidar digirin farko a wannan sashe. Kana daga bisani sami bubbar takardar shaidar digiri wato Masters ke nan, duk dai a wannan sashe na zayyane zayyane, a shekarar 1978.
A cikin watan Agustan wannan shekarar ta 1978 ya tafi aikin bautar kasa, inda yayi aiki na tsawon shekarar guda kamar yadda tsarin yake a maaikatar ayyuka da sufuri ta jihar Oyo, wanda ya kammala a shekarar 1979.
Sakamakon irin ficen dayayi fuskar aikin da yayi karatu a kai na zayyane zayyane, hakan ya sanya Jiharsa ta Kaduna, taga cewar ya dace ta dauke shi aiki, don cin gajiyar irin basirar da Allah ya bashi, fuskar ilimi. Inda a cikin watan Fabrairu na shekarar 1986, aka nada shi a matsayin kwamishinan ayyukan gona, najihar Kaduna. Mukamin daya rike na tsawon shekaru uku.
Haka nan kuma a shekarar 1988, aka sake bashi mukamin kwamishinan ayyuka da sufuri gami da gidaje na jihar ta Kaduna.
A lokacin da yake rike da wannan maaikata, kuma a matsayinsa na mai kishin ci gaba, shi ya kirkiro da shirin sanya lantarki a yankunan karkara, ko kuma garuruwa har guda 99 a jihar, kasancewar a wannan shekara ta 1988 garuruwa uku ne kacal aka hada su da bubban layin lantarki na kasa, wadanda suka kunshi garin Kaduna na, da zariya da kuma Kafanchan.
Wani abin jin dadi a nan shine, ganin yadda aka sami nasarar aiwatar da wannan tsari daya bullo da shi, a halin yanzu a nan jihar Kaduna, akwai garuruwa sama da 70 da aka hadesu da bubban layin lantarki na kasa.
Bisa ga kudurinsa na tabbatar da cewa ya bi tsari irin na demo-karadiyya, hakan ya sanya ya shiga takara, tare da yin aiki tukuru da fatan neman nasara daga Allah, kuma cikin ikonsa, uban giji ya ida nufi, inda ya fito takarar mukamin gwamna a wannan jihar ta Kaduna, inda a karshe ya zame zakara, a zaben fidda-gwani da aka yi tsakanin yan takarar mukamin gwamnan jihar, Karkashin inuwar Jam'iyyar PDP wanda zai rikewa Jam'iyyar tuta a bubban zaben da zaa yi cikin watan Afrilun wannan shekara Idan Allah ya kaimu.
Wannan nasara dai bata Arc. Namadi Sambo bace kadai, amma nasara ce ta Jam'iyyar PDP da kuma Jama'ar jihar Kaduna baki daya.
A kokarinsa kan wannan yunkuri, ya karade dukkan yankunan kananan hukumomin jihar, tare da ganawa da shugabanni, da sauran Jama'ah da rokon alfarma agare su, wanda suka amsa, kuma suka taimaka.
Bayan wannan zabe, na fida-gwani sai muka mika kai, ga uwar Jam'iyyar don aiwatar da tsare tsaren yakin neman zabe.
Ana cikin wadannan shirye shirye ne sai aka janyo hankalinmu a game da wasu rubuce rubucen batanci, da koke-koke a rebuce, gami da sharhi a game da Arc. Namadi Sambo, dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin tutar jam'iyyar PDP, daga bangarorin wasu Jama'a, wadadanda suka kuduri aniyar yin batanci a game dakyawawan kudurorin daya sanya a gaba.
Aniyar wadannan mutane ita ce, su goga wa Arc. Namadi Sambo kashin kaji, ta hanyar yi masa zuki-ta-malli, tare da abokan tafiyarsa to siyasa, a idanun Talakawa masu zabe, gami da Jami'an tsaro, wai duk da nufin ganin bai sami nasara ba a zaben gwamnan dake tafe, wanda kowa ya sani akan cewa ya kama kyakkyawar turbar samun nasarar dare-wa, akan wannan kujera a wannan shekara da muke ciki ta 2007.
A yayin da su irin wadannan mutane ke ci gaba da zagawa da irin wadannan miyagun kalamai, dake kokarin zubda mana da mutunci, hakan yasa mukaga ya dace, mu fito fili mu fayyace gaskiyar lamarin da ake ciki, ta yadda Jama'a zasu gamsu don ganin mun cimma burinmu na tabbatar da adalci.
A halin gaskiya dai Arc. Namadi Sambo, ya mallaki kamfanoni manya guda uku wadanda suka kunshi, "Coplan Associates" da "Nalado Nigeria Limited", da kuma "Manyatta Engineering Services Limited.
COPLAN ASSOCIATES, shi wannan kamfani babban aikinsa shine tuntuba da bada shawarwari, da sukahada da aikin zayyane-zayyane da kuma na injiniya, dasamar da kayyaki, da kakkafasu, da budesu, da tsara bututun mai dana iskar Gas, da bada horo, gami da tsara huldodin da sukajibanci hada hadar kudi, ta hanyar hulda da cibiyoyin kudi na kasa da kasa, wadanda suka kunshi bankin duniya, da bankin raya kasashen Afrika, da makamantansu.
Shi kuma wannan kamfani da muke zance yana tare da hukumar yiwa kamfanoni rijista, tun a shekarar 1982. Kuma ya sami nasarar gudanar da ayyuka masu daman gaske, wadanda zamu tsinto wasu daga ciki kamar haka.
(a) aikin gina katafaren filin wasa na kasa dake Abuja, da babban filin wasannin Olympics, dake iya daukar mutane dubu dari da goma, gami da manyan sassan guda uku, wadanda zasu iya daukar mutane dubu 20, da wuraren zama dubu biyar, da dakunan kwana dari biyar. Wanda ke karkashin kulawar kwamitin fadar shugaban kasa a shekarar 1993.
(b) Aikin sanya idanu ga aikin ginin babban filin wasa na kasa dake Abuja, tare da unguwar'yan wasa, duk dake garin na Abuja, a shekarar 2001, wanda yake karkashin kulawar gwamnatin tarayya.
(c) Bada shawara akan aikin gini mai hawa uku, na cibiyar bincike (CRLC) a Mabushi Abuja. Wanda ya gudana a shekarar 1997, karkashin ci biyar binciken ayyukan gona ta kasa.
(d) Tsara bada kwangilar samar da na'urar lantarki mai karfin KV330/132 gami dawasu kananan tashoshin samar da lantarki, karkashin kulawar hukumar samar da lantarki ta kasa NEPA, shikarar 2001.
(e) Aikin kafawa da sanya idanu ga aikin samar da wasu na'urorin lantarki, tare da wasu kananan tashoshi, ga sabon kamfanin samar da lantarki na kasa PHCN/Transyco, karkashin kamfanin (PHCN) da Transyco a shekarar 2002.
(f) Aikin bada shawarwari ga aikin ginin rukunin gidaje masu saukin kudi, ga kanana gami da matsakaitan maaikata a Abuja, wanda yake karkashin kulawar hukumar kula da tashoshin Jiragen ruwan Najeriya, a shekarrar 1998.
(g) Kammalawa da kumabude babban Asibitin Garin Gombe, karkashin tsohuwar hukumar rarar man petur ta kasa PTF, a shekakar 1998.
(h) Aikin fadada mashigar ruwa dake unguwar Badagry Lagos, wand ya hada, da fadada tashar jiragen ruwa, karkashin gwamnati jihar Lagos, a shekarar 1999.
(i) Tsara kauyuka akan titin Bill Clinton da titin Airport, karkashin gwamnatin tarayya, a shekarar 2002.
(j) Aikin ginin kwalejin maaikatan gwamnatin tarayya Abuja, karkashin gwamnatin tarayya a shekarar 2002.
(k) Aikin tuntuba da bada shawara ga cibiyar bada horo a kan harkar albarkatun man fetur, da Jami'ar mai da iskar Gas ta garin Warri, da bada shawarwari aikin cibiyar fasaha ta kasa dake Bonny, a 2005.
(l) Kwalejin kimiyya da fasaha a kan albarkatun mai da Iskar Gas dake Ekowe Jihar Bayelsa, akarkashin hukumar fasara raya albarkatun man fetur PTDF a shekarar 2006.
KAMFANIN NALADO NIGERIA LIMITED. Shi wannan kamfani da yayi rijista tun a shekarar 1982 da hukumar yiwa kamfanoni rijista dake Abuja, ya kware ta wadannan fannoni:
- Hada hadar mai da iskar Gas. Samar da ruwa da kwashe shara.
- Aikin injiniyan gine gine da kuma zayyane zayyane.
- Samar da lantarki, da rarrabashi.
- Kwarewa ga aikin na'urorin sanyaya wuri, da makamantansa.
- Samar da na'urorin da injina.
- Kawo wa yanzu, wannan kamfani ya aiwatar da ayyuka da dama kamar haka.
1, Samar da babban Na'urar aikin tonon kasa, dake iya yin aikin da man Diesel ko kuma lantarki, mai lamb 70117 Type zj 70d a karkashin kamfanin NPDC, wani sashe na kamfanin mai na kasa NNPC a Port-Harcourt a shekarar 2002.
2, Aikin samar da ruwa a yankunan karkara a jihar Sokoto, a karkashin tsohuwar hukumar kula da rarar man fetur ta kasa PTF, a shekarar 1998.
3, Gina cibiyar yawon shakatawa dake Ibeju-Lekki, Akodo Lagos, Karkashin gwamnatin jihar Lagos daga shekarun 1998/1999.
4, Aikin samar da ruwa a shiyya ta daya karkashin tallafin Bankin duniya, a bisa kulawar maaikatar albarkatu ruwa ta tarayya daga shekarun 1995/1998 a jiholin Borno da Niger.
5, Aikin samar da ruwa na garin Biu, a shekarar 2001.
6, Aikin ginin cibiyar shakatawa a garin Maiduguri, jihar Borno, a karkashin gwamnatin jihar Borno, a sheakarar 1995.
7, Kafa kanana da manyan cibiyoyin kara samar da karfin lantarki a Lagos, Karkashin hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa, a shekarar 1995.
8, Samarwa da kuma rarrab na'urorin lantarki na Transformer ga hukumar lantarki ta kasa NEPA, a shekara ta 2000.
Bubban Kamfani Na Uku, a Karkashin Arc. Namadi Sambo, Shi Ne Manyatta Engineering Services Limited, Wanda Yayi Rijista Da Hukumar Yiwa Kamfanoni Rijista a Ranar 5 Ga Watan Oktoba Shekarar 1998, Shi Wannan Kamfani Ya Kware Fuskar Samar Da Kayyaki ta Tudu, Da Sukar Hada Da Kayyakin Lantarki, Dana Binciken Kimiyya, Da Kayayyakin Asibiti, Dana Wasanni.
Daga Cikin Irin Ayyukan Daya Gudanar Sun Hada Da.
A, Gyaran kayyakin tsohon filin jirgin saman Kaduna, karkashin ma'aikatar ayyukan gona da albarkatun kasa ta tarayya daga shekarar 2002/2005.
B, Samar da jiragen Helkwafta masu lamba 2, ga hukumar ‘yan sanda ta Najeriya a shekarar 2005.
Kamar yadda zaa iya shaidawa, babu daga cikin ayyukan kamfanoni da aka yi a ko dai kan hanya ko kuma madatsar ruwa, kamar yadda wadancen masu yada kanzon-kurege ke bayyanawa. Kuma wadannan kamfanoni na gudanar da ayyukansu ne a bangarorin da suka yi fice a kai, kuma wadanda duk suka basu aiki sun gamsu da irin ayyukan da suka yi musu.
Bugu da kari, wadannan kamfanoni sun yi rijista da hukumar yiwa kamfanoni rijista, kana zaa iya ganin irin nasarorinsu ga masu hulda da su, don iya tantancewa akan ko kanfanonin hadin guiwa ne da nufin fadada, hada-hadar wani daban, sabanin ayyukansu na hakika, da suka sanya aka kafa kamfanonin.
Ga masu rubuce-rubucen shaci-fadi na cewa wai mai girma gwamnan jihar Kaduna Alh. Ahmed Makarfi yayi uwa- da makarbiya don tabbatar da samun nasarar Arc. Namadi Sambo a zaben fidda gwani na yan takarar gwamnan da aka kammala bada jimawa ba, a nan muna masu tabbakar musu da cewa, an gudanar da wannan zabe cikin walwala da adalci.
A nan ba wai muna nufin kare gwamna Makarfi ba ne, ta kowace irin fuska, to amma kuma muna masu nisantashi daga duk wani tunanin cewa ya tallafa ga samun nasara Arc. Namadi Sambo a wannan zaben fidda gwani.
Dalili kuwa shine Gwamna Makarfi ya tara dukkan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar daga dukkan kananan hukumomi, a jihar Kaduna, a gidan gwamnati na Hassan Usman Katsina dake kawo, inda ya tsame kansa daga goyon bayan duk wani dan takara ciki kuwa har da Arc. Namadi Sambo.
Wannan mataki ya fayyace cewa babu wani dan takara da gwamna ke marawa-baya, duk da cewa mun san cewa da dadewa Arc. Namadi Sambo ya dade yana abuta da gwamna Ahmed Makarfi to amma kuma shi ba abokin huldarsa ta kasuwanci ba ne.
Domin kuwa Arc. Namadi Sambo, ya riki mukamin kwamishina daga shekarar 1986 zuwa 1991, tsawon shekaru biyar, yayin da gwamna Makarfi kuma ya riki mukamin kwamishina daga shekarar 1994 zuwa 1997, haka nan kuma Arc. Namadi Sambo dan kasuwa ne, daya soma mallakar kamfuna daga shekarar 1982 har ya zuwa yau.
Kaga a nan, dogon batu ne tun kafin Makarfi ya zama kwamishina, kana daga bisani ya zame gwamna. To anan babu yadda zaa yi a iya kwatanta abokantakarsu da harkar kasuwanci ko muma hadin guiwa.
Wani cikakken bincike da ya shafi bukatar ruwa a zariya, wanda maiakatar albarkatun ruwa ta tarayya ta gudanar ya tabbatar da cewa bi sa ga yawan samar da birnin zariya ke kunshe da su, tana bukatar lita milyan 120 na ruwa a duk rana.
Aikin kwangilar da daya daga cikin kamfanoni mallakar Arc. Namadi Sambo ke gudanarwa mai suna NALADO NIGERIA LIMITED, daya shafi aikin samar da ruwa na zariya, ya kunshi aikin gyaran tsohuwar cibiyar samar da ruwar ta garin zariya, wanda aikin gwamnatin tarayya ne, mai lamba kamar haka, MWR/SD/197/T wanda makasudinsa shine gyara tsohon tsarin da ake da shi na asali, da zai iya samar da lita miliyan 60 na ruwa a kowace rana, kamar yadda aka bukata a shekarar 1973.
Kafin bada wannan aiki da aka yi, al'umar Zariya na samun ruwan da bai wuce lita milyan 24, ba sabili da lalacewar da cibiyar ta yi. Haka nan kuma cibiyar tsaftace ruwan tazariya bata iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, wadanda aka kafa tsakanin shekarun 1955 zuwa 1973, sabili da irin tsufan da ta yi.
A halin yanzu an kammala dukkan ayyukan da suka kamata a wannan wuri, a don haka aikin daya rage kadai shine hada lantarki, daga hukumar ko kuma kamfanin lantarki na kasa PHCN, tare da jera bututu, da ake sa ran kamfanin NALADO zai shigo da su daga Turai bada jimawa ba, don kammala aikin, wanda bisa kiyasi ya kai kashi 80, na kammaluwa.
A kokarin gwamnatin tarayya na samar da wadatacen ruwa ga al'umar zariya, ta yi kokarin gina madatsar ruwa, da hakan yazama tilas gashawo kan matsalar karancin ruwan da ake fama da shi, a dalilin hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta bada aikin ginin sabuwar madatsar ruwa da kuma kwangilar samar da sabbin na'urorin tace ruwan, wanda hakan zai tabbatar da cewa da zarar an kammala wadannan ayyuka zariya zata yi ban kwana da batun karanchin ruwa.
A kokarin hakan ya sanya maiakatar albarkatun ruwa ta tarayya, ta tallata bada aikin, kana ta amshi takardun nema, daga kamfanoni daban daban, wanda daga bisani kamfanin GILMOR NIGERIA LIMITED ya sami nasara, haka kuma a halin da ake ciki ana kan kokarin bada kwangilar samar da na'urorin tace ruwan. A don haka babu kanshin gaskiya cewa kamfanin NALADO NIGERIA LIMITED shi aka baiwa kwangilar gina wanan ruwa.
A nan ya kamata a fahimci cewar aikin gwamnatin tarayya baya da wani jibi da gwamnatin jihar Kaduna, ko kuma shi kansa gwamna Makarfi.
Bugu da kari, zamu iya fayyace cewar kamfanin NALADO NIGERIA LIMITED, ko kuma duk wani kamfani karkashin Sambo, bai amshi wani aikin da aka yi watsi da shi ba.
A ko da yaushe yakan yi kokarin kammala duk wani aikin da aka bashi, akan lokacin da aka kayyade, koda kuwa bai sami wata riba a kai ba.
A yayin gwamnatin Makarfi kuwa aikin da aka baiwa kamfanin NALADO NIGERIA LIMITED a gwamnatin jihar Kaduna, ya soma ne a shakarar 2005, kuma aikin shi ne na gyaran filin wasa na RANCHERS BEES, wanda tuni aka kammala kuma mai girma shugaban kasa ya bude shi.
Haka kuma an biya kudin aikin bayan bin dukkan ka'idojin da suka kamata, kamin ya sami amincewar Injiniyoyi daga maaikatar ayyuka ta jihar Kaduna, da suka kulada aikin. A don haka shaci-fadin da ake yi na kudin aikin wani aiki ne na yan ingizamai-kantin-ruwa.
WADANNAN NA DAGA CIKIN KADAN DAGA AYYUKAN KANFANIN NALADO, DA SUKA HADA DA,.......
1,aikin gyaran dandallin Murtala dake Kaduna, wanda aka tallata bada aikin, bisa ga irin kaidojin da gwamnati ta shinfida, kana kamfanin NALADO NIGERIA LIMITED miyayi nasarar samu, a nan kamfahin na NALADO NIGERIA LIMITED am mika mata izinin fara gudannar da aikin ne kawai ya dauki wani bangare ne kawai na aikin, amma ba wai yana ikirarin cewa ya kammala aikin baki daya bane.
2, Sai kuma aikin gina filin wasa na zariya, wanda shima aka tallata shi, kuma bayan gwamnati ta gama shimfida ka'idojinta na kai, sai aka baiwa kamfanin da yayi nasara, wanda a hallin yanzu aikin ya tasamma kashi 45 na kammaluwa, a cikin watanni biyu.
3, Samar da na'urar samar da lantarki mai karfin KVA 750, a cibiyar samar da ruwa ta Zonkwa a Monchok, wanda aiki ne na bankin duniya wanda bayan an tallatashi sai kamfanin NALADO ya sami nasara.
Baya ga wannan, aikin gyaran filin wasa na garin Kafanchan kuwa an bada shi ne ga wani kamfani mai suna B&D Limited, kamfanin gine gine, mai helkwata a Abuja, wanda babu abin daya hadasu da wani kamfanin Arc. Namadi Sambo.
Yana da matukar muhimanci a fahimci cewa kamfanonin NALADO NIGERIA LIMITED, DA COPLAN ASSOCIATES, DA KUMA MANYATTA ENGINEERING SERVICES LIMITED, tsawon shekaru sun dade da kwarewa ga ayyukansu, kuma sun yi fice a fadin najeriya, a manyan kamfanoni, kuma bisa ga irin wannan fice da suka yi ne, ya sanya suke samun ayyuka dagga Bankin Duniya, da gwamnatin tarayya dana jihohi tare da samu ayyuka daga bangarori masu zaman kansu.
Wasu rubuce-rubuce da aka yi ta yi, bada jimawa ba, inda akan yi amfani da banbancin addini don ganin cewa an sami nasara ga zaben fidda gwani na yan takarar gwamna da aka kammala kwanakin baya, ta yadda ‘yan ingiza-mai kantu-ruwa, ke kokarin ganin sun zafafa lamura fuskar siyasa, anan muna masu farin cikin sanar da cewa Arc. Namadi Sambo musulmi ne, kuma bai taba taka wata rawa ta tada hatsaniya a kowane bangare na kasa ko na duniya ba, kuma shi bai taba nuna wata kyamata ga wani addini ba.
Shi mutum ne da ako yaushe yake mai yin imani da koyarwar addini a kan zaman lafiya tare da bin tafarkin ci gaba da samar da zaman lumana tsakanin al'ummar musulmi dana kiristan jihar Kaduna.
Haka nan kuma bisa wasu yan takardu masu nasaba da addini da wa su mutane suka rika rarrabawa wadda ake tunanin cewa wai wasu na hannun daman Arc. Namadi Sambo ne suka rika rabawa, a nan muna sanar da cewa baya da hannu kuma baya da masaniya a kai, ko kuma wani a cikin kwamitinsa na yakin neman zabe.
A nan ai zaa iya tabbatar da hakan a cikin jawabin da abokin takararsa yayi bayan sanar da sakamakon zagaye na biyu na zaben fida gwani, inda yace "Na tabbatar da cewa baka da masaniya a game da takardun da aka rarraba, amma kuma a nawa bangaren zan bi diddigi har sai na gano inda suka fito".
Anan muna masu amfani da wannan dama wajen yin kira ga cikakkun yan siyasa su kaucewa duk wani nau'in nuna banbancin addini da kuma tashin hankali don ganin jihar nan ta ci gaba da bunkasa.
Wannan kira yayi daidai da raayin sarakuna, da kuma shugabannin da muke da su a wannan jihar ta Kaduna. Wadanda a kullum burinsu shine a zauna lafiya, don cigaban al'umma baki-daya.
Bisa ga wadannan bayanai da muka zayyana, tare da sanin cewa shi fa Arc. Namadi Sambo ya riki mukamin kwamishina har na tsawon shekaru biyar a wannan jihar ta Kaduna, kuma ya tabayin takarar neman muka min gwamna, tare da gwamna Makarfi a tsohuwar Jam'iyyar DPN, a nan zamu san cewa Arc. Namadi Sambo, mutum ne daya dogara da kansa, wanda ke da bukatar kyakkyawar rayuwa dakuma gudanar da aiki don ci gaban jihar Kaduna.
A dalilin irin wadannan batutuwa dake tasowa ne ya sanya muka rubuta wadannan bayanai don yin gyara akan irin kalaman da ake yi a kan Arc. Namadi Sambo, daga yan adawa, wadanda burinsu shine su rusa duk kyakkyawan ginin da yayi.
A don haka mun kuduri aniyar fidda dukkan bayanai da nasarorin daya samu a fili, don ci gaban jihar Kaduna, tare da sabon gwamna In Sha Allah, mai burin ganin ya ciyar da jihar Kaduna gaba.
A bisa ga al'ada irin ta demokaradiyya dai kowane dan takara kan zayyana kudurori gami da alkwuran alheri da yakan dauka ga Jama'arsa.
Hakan ne ya tado da ayar tambaya, akan ko wadanne irin kudurori, shi wannan bawan Allah, wato Arc. Mohammed Namadi Sambo ke da su, ga al'ummar wannan jihar ta Kaduna, Idan Allah ya sa aka kai ga nasara.
A kowace karamar hukuma daga cikin guda 23 da muke da su a wannan jihar ta Kaduna, lokacin yakin neman zabe, karon farko, ya bayyana kadan daga cikin irin wadannan kyawawan kudurori da alkawura, kamar haka.
1. Bada ilimin firamare kyauta
2. Raga talauci
3. Bunkasa rayuwar matasa
4. Samar da ababen more rayuwa
5. Inganta tsarin kiwon lafiya
6. Bunkasa aikin gona
7. Samar da karin guraben ayyukan yi, ta hanyar kafa kanana da kuma manyan masanantu.
8. Samar da gidaje ga marasa karfi
9. Bunkasa yankunan karkara, ya zuwa matsayi irin na zamani
10. Inganta jin dadin ma'aikata, da masu amsan fansho
11. Kyautata tsarin ilimi baki daya
Wadannan kadan ne, daga cikin tarihin rayuwa, da kuma gwagwarmaya, don fayyace gaskiyar lamari, a game da tauraron dan takarar gwamnan jihar Kaduna, karkashin inuwar Jam'iyyar PDP Arc. Mohammed Namadi Sambo.